Neman dorewar dimokradiyya a Tunisiya
December 23, 2014Shugaba Beji Caid Elsibsi da Moncef Marzouki da aka kayar zaben shugaban kasar sun bukaci hadin kan magoya byansu da al'ummar kasar ce da nufin ganin sun hade waje guda don ciyar kasar gaba. Wannan kira na shugabannin biyu ya zo ne bayan da a hukumance aka bayyana Mr. Essebsi a matsayin wanda ya samu nasara a zagaye na biyu na zaben.
Bangarorin biyu dai suka ce wannan kira ya zama wajibi don ganin kasar ta samu cigaba mai mai'ana da duma samun sukunin dorewar mulkin dimokradiyya wanda ke cikin jerin abubuwan da suka sanya aka yi juyin juya halin da ya kifar da gwamnatin Zainul Abideen Bn Ali a shekarun da suka gabata.
Da ya ke jawabi ga al'ummar kasar shugaban kasar mai barin gado kana wanda ya sha kaye a zaben na ranar Lahadi Moncef Marzouki cewa ya yi "wannan shi ne tafarkin dimokiradiyya na farko da muka fara gogayya da shi a kasarmu, don haka bai kamata mu bata rawarmu da tsalle ba ta hanyar kin amincewa da sakamakon da akwatunan zabe suka nuna. Ina kira ga magoya bayana da yan kasa da kowa ya kai zuciya nesa kana a bawa sabon shugaba cikakken hadin kai"
Shi kuwa sabon shugaban mai jiran gado Beji Caid Essebsibayan godiya ga abokin takararsa yayi kan irin dattakun da ya nuna sakamakon taya shi murna da ya yi kan nasarar kammala wannan rukunin karshe na komawa kasar kan tafarkin dimokiradiya inda ya kara da cewar ''ina kara tabbatar muku da cewa zan rungumi kowa mu tafi tare. Ba abin da ya rage mana bayan gama zabe illa mu fuskanci kyautata gaba."
Kasashen duniya dai musamman ma na yankin gabas ta tsakiya sun taya Tunisiya murnar komawa kan tafarkin dimokradiyya wanda da dama ke cewar boren da suka yi da ya haifar da juyin juya hali ba fadi kasa banza ba.