Neman ceto yarjejeniyar tsagaita wutar Ukraine | Labarai | DW | 04.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Neman ceto yarjejeniyar tsagaita wutar Ukraine

Kasashen duniya ciki kuwa har da Amirka sun fara yin matsin lamba ga Rasha na tabbatar da dorewar yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Ukraine da 'yan aware.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amrika Jen Psaki ta ce dole ne Rasha ta yi amfani da matsyinta tare da irin tasirin da take da shi kan 'yan awaren Ukraine din don dakile shigar makamai kasar da nufin kawo karshen tashin hankali.

A 'yan kwanakin nan dai rikici tsakanin sojin Ukraine da 'yan awaren da ke biyayya ga Moscow ya yi kamari don ko a jiya ma sai da suka tafaka kazamin fada a wani yukuri da bangarorin biyu ke yi na ganin sun karbe iko da filin jirgin saman da ke Donesk wanda ke da muhimmanci gaske ga rajin da 'yan awaren ke yi na samun 'yancin kai.