1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman ceto yankin Arewa daga mawuyacin hali

January 24, 2013

Wata kungiya mai rajin saita alkibilar arewacin Najeriya ta shirya taro na kwanaki biyu a kano, da nufin ceto yankin daga halin fatara da rashin tsaro da yake ciki. Sai dai matasa suka ce manyan arewa ne matsalar yankin.

https://p.dw.com/p/17R5O
Hoto: picture-alliance/dpa

Galibin manyan tsofoffin shugabannin kasar da kuma gwamnoni ba su sami damar halarta ba. Amma duk kuma an samu fuskokin manyan jiga jigan yankin na Arewa da suka rike mukamai daban daban. An dai shirya gabatar da taron ne a dakin taro na Central hotel dake jihar ta kano, amma sakamakon dalilan tsaro aka sauya bigiren taron zuwa fadar gwamnatin jihar ta Africa House.

A Lokacin da yake gabatar da makala yayin taron Alhaji Usman Faruk tsohon gwamnan jihar Arewa maso Yammacin Najeriya ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kafa kwamitin bincike domin gano musababbin rikice rikicen da ya addabi yankin. Haka kuma ya zargi gwamnatin tarayya da nuna halin ko in kula da rikicin da yankin ya afka tun daga shekara ta 2001. Kazalika ya nemi da aka kafa hukuma da za ta farfado da yankin kwatankwacin irin ta yankin Niger Delta. A lokacin da ya yi wa wakilin Deutsche Welle bayani sakataren kungiyar da ta shirya taron Dr Sadiq Umar Abubakar Gombe ya bayyana cewar  makasudin taron shi ne ceto yankin daga halin ha'ula'i da ya fada.

Wahlen Nigeria Genral Muhammadu Buhari
Janar Buhari ne ya jagoranci Taron na KanoHoto: AP

Injiniya Magaji Da'u Aliyu da ke zaman mai fashin baki akan al'amuran yau da kullum ya bayyana cewar abu ne mai wuya taro irin wannan ya haifi da mai ido. Ya na mai cewa galibin manyan baki a yayin taron su ne ke dankwafe yunkurin ci gaban yankin. Su ma Kungiyoyin matasa da na dalibai da dama da suka halarci taron, sun koka bisa yadda suke ganin ba kasafai taruka irin wannan suke amfana wani abin azo a gani ba. Shugaban kungiyar dalibai na jami'ar Bayero dake kano Sani Sadiq Ibrahim yace 'yan arewa sune matsalar yankin.

Poliobekämpfung Nordnigeria
Polio na daga cikin cututtukan da suka addabi ArewaHoto: Thomas Kruchem

To amma Danlami Hamza wanda tsohon dan majalisar wakilai ta Tarayyar Najeriya na ganin cewar taron kan iya zama wani mataki na kamo bakin matsalar dake addabar yankin, musamman yadda aka tabo batun ilimi dake zaman kashin bayan cigaba. Da farko dai an shirya cewar tsohon shugaban kasar Najeriya janar Yakubu Gawon shi ne zai jagorancin taron. Amma rashin zuwansa ya sa aka mika jagoranci ga janar Muhammadu Buhari, wanda shine kadai tsohon shugaban kasa daga cikin tsoffin shugabannin kasar 4 da suka fito daga yankin kuma aka mika musu goron gayyata zuwa taron.

Rahotanni cikin sauti na kasa

Mawallafi: Nasir Salisu Zango
Edita: Mouhamadou Awal