Neman agaji ga ′yan Siriya | Labarai | DW | 28.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Neman agaji ga 'yan Siriya

Ministan harkokin kasashen ketare na nan Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bukaci kasashen duniya da su zuba jari a kasashen da ke daukar bakuncin 'yan gudun hijirar Siriya.

Steinmeier ya bayyana haka ne yayin wani taro na yinin guda da ya shirya a nan Jamus domin rage wahalhalun da 'yan gudun hijirar Siriyan ke fama da su da ma su kansu kasashsne da ke karbar bakuncinsu, inda ya ce akwai bukatar zuba jari a asibitoci da makarantu da fannin ruwan sha da ma na skwwashe shara a kasashen da ke daukar dawainiyar ta su. Tuni dai kasar Lebanon da ke daukar bakuncin sama da miliyan guda na 'yan gudun hijirar ta ce sun mata yawa, kuma tana bukatar tallafi daga al'ummomin kasa da kasa. Taron dai na samun halartar da ministocin harkokin kasashen ketare na kasashe sama da 40.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane