NDP ta tsayar da Konadu Rawlings takara | Siyasa | DW | 04.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

NDP ta tsayar da Konadu Rawlings takara

Jam'iyyar National Democratic Party a kasar Ghana ta bayyana Nana Konadu Agyemang Rawlings a matsayin wadda za ta tsaya mata takarar shugabancin kasar a zabe mai zuwa.

Nana Konadu Rawlings yayin kaddamar da ita a matsayin 'yar takarar shugabancin kasa

Nana Konadu Rawlings yayin kaddamar da ita a matsayin 'yar takarar shugabancin kasa

Nana Konadu Agyemang Rawlings dai ta kasance uwargida ga tsohon shugaban kasar Ghana Jerry Rawlings. Matakin jam'iyyar ta NDP dai na zuwa ne yayin da Konadu Rawlings ke cike da fatan zama mace ta farko da za ta rike madafun ikon kasar. A jawabanta daban-daban Konedu Rawlings ta sha nanata cewar lokaci ya yi da wata mace mai kamar maza ya dace ta mulki kasar ta Ghana. Bayan da jam'iyyar tata wadda kuma ita ce ta kafa ta wato NDP ta tsayar da ita takara, Nana Konadu Agyemang Rawlings ta ce:

Ghana Nana Konadu NDP Partei Kongress

Jiga-jigan NDP yayin babban taron jam'iyyar

"Muna son ganin mun kawo gaskiya da taka tsan-tsan wajen alkinta dukiyar kasa, mutane na son yin magana a kan gaskiya da nuna dattaku wajen kare dukiyar al'umma a lokacin da suka dulmiya hannayen su cikin dukiyar al'ummar kasar Ghana, to amma idan duk muna son magance hakan da kanmu, ya zama dole mu fadaka."

Zabe karo na biyu

An dai taba zabar Nana Konedu Rwalings a matsayin 'yar takarar shugabancin kasar Ghana a karkashin jam'iyyar ta NDP a babban zaben kasar a sheakara ta 2012, to amma ta gaza wajen kare dama ta wanda hakan ya sanya aka yi waje da ita. Mai shekaru 67 a duniya, yanzu haka Konadu Rawlings na fatan ganin ta doke shugaban kasar mai ci wato John Mahama musamman ta hanyar shan alwashin yin yaki da cin hanci da rashawa.

Ghana Nana Konadu NDP Partei Kongress

Tsohon shugaban Ghana Jerry Rawlings a zauren babban taron jam'iyyar NDP

Tun dai a shekara ta 2012 Madam Nana Konadu ta bar jam'iyyar NDP bayan da ta gaza doke dan takarar shugabancin kasar na wancan lokacin wato marigayi John Ata Mills, daga nan kuma ta yi wuf ta kafa wani bangare a cikin jam'iyyar da ya dare ta hanyar janyo mambobi daga wasu jam'iyyun kasar. Bayyanar mijinta wato Jerry Rawlings wanda ya taba zama shugaban kasar ta Ghana ta taka muhimmiyar rawa a babban taron jam'iyyar.

Tasirin Jerry Rawlings

Bayyanar Jerry Rawlings tare da ma taimakawa mai dakin nasa ka iya kasancewa wani muhimmin matakin ta zai iya taimaka mata wajen lashe kuri'un al'ummar Ghana, ko da yake ba lallai ne hakan ya yi tasiri ba. Tuni dai Madam Nana Konedu ta bayyana cewar jam'iyyarta na da wani babban sako na fata ga al'ummar Ghana musamman makoma ta gari da kuma samun ci-gaban al'amura a kasar baki daya.

Sauti da bidiyo akan labarin