1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nazari game da dambaruwar siyasar Nijar

February 11, 2014

Takaddamar shugabanci a jam'iyar CDS Rahama mai adawa a Nijar, na daga cikin rigingimun siyasar baya bayannan da kasar ke fama dashi.

https://p.dw.com/p/1B73t
Mahamane Ousmane 1995 Präsident Niger
Hoto: picture-alliance/dpa

A wannan Talatar (11. 02. 2014) ce, kotun kolin karya shari'a a Jamhuriyar Nijar, wato Cour de Cassation, ta sake zaman shari'ar rikicin jam'iyar CDS Rahama da ke adawa, tsakanin ministan albakatun Gona Abdu Labo, da shugaban jami'yar Mahaman Usman.

Wannan takaddamar ta ake kunno kai ne a yayin da batun kudaden da tsohon shugaban kasar Tandja Mamadou ya bari bayan kifar da mulki, ke ci gaba da daukar hankalin jama'a, inda tsohon shugaban kasar ya baiyana bankin raya kasashen Musulmi ya taimaka ma Nijar don gudanar da aikin babban Dam, wato Marage Candaji.

Mawallafi : Mamman Kanta
Edita : Saleh Umar Saleh