Navy Pillay ta nemi a kai dauki a Bangui | Labarai | DW | 21.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Navy Pillay ta nemi a kai dauki a Bangui

Hukumar kare hakin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci al'ummomin duniya da su gaggauta yin wani abu domin kawo karshen zubar da jini a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Babbar jami'ar hukumar d ake ziyara a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar Navi Pillay ta shaida wa manema labrai a Bangui babban birnin kasar cewa kiyayyar da ke tsakanin mabiya addinin Muslunci da Kirista ta kai intaha a kasar. Ta ce har yanzu akwai rahotanni da ke nuni da cewa ana azabtar da mutane da kashe yara kanana tare kuma da cin naman mutane a wannan kasa da ke fama da rikicin addini.

Pillay ta kara da cewa babu doka da oda a kasar inda sojojin yankin kudancin Afirka 6000 da kuma sojojin kasar Faransa 2000 ne kawai ke kokarin taimakawa wajen shawo kan rikicin ta da bayyana da wani yaki da ya koma ya zuwa kokarin shafe al'ummar Musulmi tsiraru dake kasar da yaki ya daidaita.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohamadou Auwal Balarabe