1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Naurar leken asirin koriya ta Arewa ta gamu da cikas

Binta Aliyu Zurmi
May 31, 2023

Koriya ta Arewa ta yi yunkurin kaddamar da tauraron dan Adama a karon farko don leken asirin Amirka, amma ba ta yi nasara ba inda naurar ta fada cikin teku.

https://p.dw.com/p/4RzUR
South Korea Koreas Tensions
Hoto: South Korea Defense Ministry/AP/picture alliance

Koriya ta Arewa  ba ta da tauraron dan Adam ko daya a sararin samaniya. Sai dai Shugaba Kim Jong Un ya jima da mayar da samar da tauraron dan adam na leken asirin soja a matsayin babban ginshiki na gwamnatinsa, a lokacin da sojojin Amirka da na Koriya ta Kudu ke ci gaba da atisayen hadin gwiwa.

Koriya da Kudu da Japan da Amirka sun yi Allah wadai da wannan gwajin wanda suka ce ya saba wadokokin Majalisar Dinkin Duniya da ya haramta wa Pyongyang gwajin makamai masu linzami.

Koriya ta Arewa ta sha alwashin sake gyara tauraron tare da neman nasarar harba shi a sararin samaniya nan bada jimawa ba bayan ta amince cewa na'urar na cike da kura-kurai.