1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Na'urar busar da kayan miya a Najeriya

Ahmed Salisu
August 10, 2017

Wani matashi Abujan Najeriya ya sami nasar samar da wata na'urar busar da duk wasu danyun kaya da suka hada da albasa da tumatir da attaruhu domin alkintasu tare da bunkasa harkokin safarar su zuwa wasu gurare.

https://p.dw.com/p/2i2Ky
Bildergalerie Bioanbau in Uganda Bio-Tomaten
Hoto: DW/L. Schadomsky

Ita dai wannan na'ura da matashin ya kirkiro kan taimaka wajen busar da kayan gwari da nufin adana su don gudun kada su lalace. Kazalika na'urar wacce ta ke amfani da hasken rana yanzu haka an fara amfani da ita a tsakanin masu amfani da kayan gwari a Najeriya. Kusan dai kimanin shekaru sama da uku kenan da suka gabata matashin mai suna Isyaku Mamman ya yunkuro domin kawo wani babban sauyi ga yadda masu safarar kayayyakin gwari daga wannan gari zuwa wancan.

A hirarsa da DW, matashin ya ce kamfar wutar lantarki wadda za a yi amfani da ita wajen adana kayan a furunji ne ya sanya shi tunanin samar da wannan na'ura idan ya kara da cewar baya ga kayan miya, wannan na'ura da ya kirkira kan iya taimakawa wajen busar da duk wani danye kaya da ka iya lalacewa idan ba alkinta shi ba. 

Matashin ba wai kawai ya tsaya ga nan ba har ma matasa ya ke nunawa irin yadda za su tsaya da kafafun su. A share guda kuma ya gayawa DW cewar burinsa shi ne ya wayi gari  masu safarrar kayan gwari su dinga alkinta kayayyankin su kamar yadda ya dace domin kara bunkasa yanayin harkokin kayan gwari a Najeriya.