1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutum na farko ya mutu daga nau'in omicron

Ramatu Garba Baba
December 13, 2021

Nau'in cutar corona mai suna omicron ya kashe mutum na farko a kasar Britaniya kamar yadda firaiministan kasar Boris Johnson ya tabbatar ma manema labarai.

https://p.dw.com/p/44Bxs
UK Covid-19 | Intensivstation
Hoto: Neil Hall/AFP/Getty Images

Firaiministan Britaniya Boris Johnson, ya ce an sami mutum na farko da nau'in omicron ya kashe a cikin kasar. Da ya ke jawabi ga manema labarai, Mista Johnson ya ce, bayan nuna alhini ga iyalan mamacin, ya ce, wannan ya kara tabbatar musu da cewa, ba za a yi sake a yakar sabon nau'in cutar ba, ganin irin haduran da masana suka riga suka ce na tattare da nau'in na omicron.

Tun dai bayan gano sabon nau'in cutar da aka yi a karon farko a Afrika ta Kudu, Britaniyan ta dauki matakai na hana shiga kasar daga duk wata kasar da omicron ya riga ya bulla, kafin daga bisani, aka gano cutar ta riga ta bulla a kasar inda a wannan Litinin tayi sanadiyar mutuwar mutum daya. Rahotanni sun nuna cewa, omicron ya ci gaba da yaduwa a sassan duniya sannu a hankali, inda Chaina da Hungary suka tabbatar da bullarsa a cikin kasashen a wannan Litinin.