NATO za ta kara yawan dakarunta a kasashen gabashin Turai | Labarai | DW | 08.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

NATO za ta kara yawan dakarunta a kasashen gabashin Turai

Kungiyar ta kawancen tsaro za ta dauki wannan mataki ne don dakile barazanar da kawayenta na gabashin Turai ke fuskanta daga Rasha.

NATO-Verteidigungsminister in Brüssel

Ministocin tsaron kasashen kungiyar NATO a Brussels

Kasashen Jamus da Amirka na son a girke karin dakarun kungiyar kawancen tsaro ta NATO cikin kasashe membobinta da ke gabashin Turai. Rahotanni sun ce ana iya tura daruruwan sojoji da za su ba da horo a kasashen Poland da Latviya da Estoniya da kuma Litawun wadanda ke fuskantar barazana daga Rasha dangane da rikicin kasar Ukraine.

A dangane da rikicin kasar Siriya kuwa inda yanzu haka Rasha take luguden wuta a kan mayakan IS, kungiyar ta NATO ta ce tana kuma tunanin karfafa yawan sojojinta a kasashe irinsu Turkiya. Babban sakataren kungiyar Jens Stoltenberg ya fadi hakan lokacin bude taron ministocin tsaro na kawance a birnin Brussels, inda ma ya kara da cewa.

"Muna fuskantar kalubale daga bangarori daban-daban. Ga rikice-rikice da rashin tsaro da kuma matsalar 'yan gudun hijira sakamakon rikicin a kasashen kudancinmu. NATO tana daukar matakan bai-daya na karfafa tsaronta mafi girma tun kawo karshen yakin cacar baka."