NATO ta gargadi ′yan awaren Ukraine | Labarai | DW | 26.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

NATO ta gargadi 'yan awaren Ukraine

Kungiyar tsaro ta NATO ta ce ba za ta amince da duk wani yunkuri da 'yan awaren Ukraine za su yi ba na kara girman wuraren da suka mamaye a ba.

Babban sakataren kungiyar Jens Stoltenberg ne ya yi wannan gargadin dazu bayan wani taro da ya yi da firaminsitan Italiya Matteo Renzi, inda ya ke cewar ya zama wajibi 'yan awaren su janye kayan yakinsu a inda suka ja daga da dakarun Ukraine a gabashin kasar.

Kalaman na Mr. Stoltenberg na zuwa ne bayan da Kiev ta ayyana fara janye manyan makaman yakinta daga fagen daga a dazu, matakin da ya ce abu ne mai kyau kuma hakan zai taimaka wajen samun zaman lafiya da mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarorin biyu suka amince da ita a kwanakin baya.