1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kugiyar Tsaro ta NATO ta cika shekaru 70 da kafuwa

Hasselbach, Christoph ZMA
April 4, 2019

A ranar 4 ga watan Afrilun shekara ta 1949 kasashen Turai 12 da Amurka suka kafa kungiyar tsaron arewacin tekun Atlantika wato NATO. Sai dai yanzu shugaba Donald Trump na Amurka na dasa ayar tambaya a kan kungiyar.

https://p.dw.com/p/3GGGF
Brüssel Nato-Hauptquartier
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Warnand

Tsohon babban magatakardar kungiyar na farko Lord Hastings Ismay na Birtaniya, ya bayyana cewar an kafa NATO ne da nufin kawar da Tarayyar Soviet, janyo Amurka a jiki tare da rage kaifin Jamus. Furucin ya fito ne jim kadan bayan yakin duniya na biyu, lokacin da kuma kusan rabin gabashin Turai ke karkashin ikon Tarayyar ta Soviet, ciki har da Jamus ta Gabas. Sannan ne Amurka ta fara tunanin ko ta bar Turan ta karata, sai dai kuma hakan na nufin karawa Tarayyar Soviet din madafan iko.  An samu matsalar sabanin ra'ayi da yakin cacar baka na sama da shekaru 40. An samu tashin jijiyar wuya, sai dai lamura sun daidaita. A kan haka ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattauna batun kwance damarar yaki da Tarayyar Soviet a shekara ta 1988 tsohon shugaban Amurka Ronald Reagan ya ce:
"Da farko za mu sanya fifiko wajen tabbatar da dorewar kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Turai da arewacin Amurka. Babu wata yarjejeniya da za mu shiga da Tarayyar Soviet da za ta sa mu salwantar da muradunmu na wannan hadaka.''