NATO na shirin tura sojojinta Afganistan | Labarai | DW | 11.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

NATO na shirin tura sojojinta Afganistan

Sakataren Janar na kungiyar tsaro ta NATO Mr. Jens Stoltenberg, ya ce akwai yuwar mambobin kungiyar su cimma matsaya kan shiga yaki da kungiyar IS a Afganistan ba tare da sauya matsayar kungiyar ba.

Ana fata dai wannan mataki na shiga yaki da kungiyar IS da kungiyar NATO ke shirin yi, ka iya jawo zazzafar muhawara na amincewa kudurin ko akasin haka kamin taron shuwagabannin kasashe mambobin kungiyar a ranar 25 ga watan Mayu shekara ta 2017. To sai dai Mr. Jens ya jadda da yunkurin shiga yakin ba zai sauya fasalin NATO na dabarun yaki da take yi da mayakan ba.

Amma bayan ganawar sakataren kungiyar da shugabar gwamnatin Jamus a birnin Berlin, Angela Merkel ta nuna matsayar ta na jagorantar horasda sojojin NATO a arewacin Afganistan, amma ta nuna shakku na kara girke wasu sojojin kasar ta a arewacin Afganistan.

"Ba na tsammin Jamus za ta kasansce na farko da zata kara tsugunarda sojojinta a Afganistan, abu mafi mahimmanci shi ne ba da karfi wajen tabbacin wanzar da zaman lafiya a arewacin Afganistan."

Dama dai kasar Jamus na cikin kasashe da ke kan gaba a cikin masu ba da gudummuwa mai karfi a cikin kungiyar NATO, inda Jamus ke da yawan sojoji kimanin 964.