NATO na kara daukan matakan inganta tsaro a Iraki | Labarai | DW | 15.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

NATO na kara daukan matakan inganta tsaro a Iraki

Kungiyar tsaro ta NATO ta dauki aniyar fadada ayyukan sojojin kungiyar zuwa kasar Iraki,a cikin shirye-shiryen farfado da kasar ta hanyar ginin makarantu da kuma sansanin horas da aikin sojoji.

Sakataren kungiyar ta tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya sanar da cewar kungiyar za ta yi nasara, sai dai bai bayyana in da za a gudanar da ayyukan ba da kuma adadin jami'an tsaron kungiyar da za su gabatar da ayyukan ba kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya sanar.