1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO: Duniya na bukatar jagorancin Jamus

Abdullahi Tanko Bala
June 23, 2020

Sakataren kungiyar kawancen tsaro ta NATO Jens Stoltenberg yace duniya na bukatar salon shugabanci irin na Jamus

https://p.dw.com/p/3eEkH
Großbritannien NATO Gipfel | Merkel und Trump
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Babban sakataren kungiyar kawancen tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya jaddada muhimmancin salon shugabancin Jamus tare da sukar matakin shugaban Amirka Donald Trump na janye sojojin Amirka 9500 daga jamus.

Stoltenberg wanda ya baiyana haka a wata hira ta musamman da tashar DW yace duniya na bukatar salon shugabanci irin na Jamus.

Yace ana bukatar Jamus ta taka muhimmiyar rawa  saboda muhimmancinta da kuma kasancewarta kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Turai.

Stoltenberg yace ya yi magana da Trump game da matakin inda ya bukace shi ya bar sojojin Amirka a nahiyar Turai, yana mai cewa hakan na da muhimmanci ga tarayyar Turai da kuma ita kanta Amirka.