NATO ba zata iya karya lagwan Taliban a Afghanistan | Labarai | DW | 01.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

NATO ba zata iya karya lagwan Taliban a Afghanistan

Kungiyar tsaro ta NATO ta ce ba ta da yawan sojojin da take bukata a Afghanistan don samun galaba nan ba da dadewa ba akan mayakan Taliban. A saboda haka a cikin watanni masu zuwa dakarun kiyaye zaman lafiya na rundunar ISAF zasu mayar da hankalin su akan aikin sake gina Afghanistan, inji kwamandan NATO Janar David Richards. A hira da jaridar Financial Times, janar din ya ce ´yan Afghanistan ka iya amincewa da rundunar ISAF da gwamnati ko da ba´a kara yawan sojoji ba. a lokaci daya janar Richards ya hakikance cewa a watannin da suka wuce dakarun sa sun taimaka wajen daidaita harkokin tsaro a Afghanistan.