Nasarorin dan jarida Boniface Mwangi a Kenya | Himma dai Matasa | DW | 09.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Nasarorin dan jarida Boniface Mwangi a Kenya

Mwangi ya lashe kyaututtuka da dama, sannan kuma ya yi kokarin samar da cibiyar damar nuna rashin jin dadinsa ga yadda al'amuran siyasa ke gudana a Kenyan.

Hotuna irin na fitattun masu fafutuka ne ke yi ma maraba da zarar ka shiga harabar cibiyar PAWA 254, inda nan ne matasan Kenya da ke da sha'awar siyasa kan haduwa don tattaunawa kan al'amura da dama. Cibiyar PAWA 254 wadda Boniface Mwangi ya kafa na amfani da kafofin sadarwa na zamani, domin hada kan al'umma wajen yakar al'mundahana da kudaden al'umma da kuma son kai.

"Lokacin da na fara a matsayin dan fafutuka ni kadai ne. Na fara aiki da zane-zane sannan na fara sana'ar daukar hoto kafin na zamo dan fafutuka, wanda ke dogaro da kansa. Na lura cewa idan aka samu irina a cikin al'umma suka hada kai da saura to za mu iya samar da kungiya.''

Yanzu haka dai yana da mabiya kimanin 27.000 a shafinsa na Twitta. Boniface mutum ne da ya yi fice wajan yin maganganu a kan abubuwa masu sarkakiya da kuma fitowa karara ya soki gwamnati. Mai shekaru 32 a duniya Boniface, ba wai kawai yana jagorantar tattaunawa ba ne a cibiyar ta PAWA 254 ya kan ma jagoranci gudanar da zanga-zanga.

"Zanga-zangar da ba za mu manta da ita ba, ita ce mamaye wata makaranta mai suna Lanala primary mataimakin shugaban kasa ne ya kwace filin wasa na makarantar don gina wajen ajiye motoci. Tare da yara 'yan makarantar mun yi kokarin karbe wajen, an jibge 'yan sanda dauke da makamai sun kuma fesa mana hayaki mai sa hawaye, amma duk da haka yaran sun jajirce sun nuna juriya har sai da ya dawo da filin wasan.''


Ko da a wajen Kenya ma, fafutukar da Boniface ke yi ta shara. Sarah Mallia da ke da shekaru 26 a duniya 'yar kasar Malta ce wadda ta nemi yin aiki da kungiyar PAWA da ya ke jagoranta bayan da ta kalli wani labari a kan kungiyar. Shekaru biyu da suka gabata ta fara aiki da kungiyar a matsayin mai sanin makamar aiki. Yanzu kuwa an dauke ta aiki a wajen.

"Duka aikin da muke yi a nan na da alaka da fafutuka, misali amafani da kafafen sada zumunta na zamani, da ma yadda zaka yi amfani da su domin tattaunawa kan rashin adalcin da ake yi a Kenya da kuma kawo sauyi. Galibin horon da muke bayarwa a kan wannan alkibla ne."

Kimanin matasa 100,000 ne suka amfana da horon da kungiyar ta PAWA ke bayarwa, misali taron "Team Courage", wanda suke yi kowanne mako da maraice kuma a cewar Mallia, galibi masu zuwa taron na zuwa ne saboda Boniface Mwangi.

''A ganina shi mutum ne abin koyi ga matasa a fannin kauracewa yin abin da bai dace ba da kuma rungumar abu mai kyau. Abin koyi ga wadanda ke son ganin an samu chanji a kasarsu."

A nasa bangaren Mwangi na da ra'ayin cewa fafutuka a kungiyarsu ta Pawa 254 yanzu suka fara.

 

"A gaba, zan so ace na taka muhimmiyar rawa a bangaren gwamnatin kasar nan, ko kuma in samu wani gurbi ko mukami na gwamnati inda zan taka rawar da ta dace dangane da aikin da na ke yanzu.''

Kafin lokacin da mafarkin Boniface zai tabbata dai, bai taba barin duk wata dama ta kubuce masa ba. Da karfin fada a jin da ya ke da shi yana fatan sauya tunanin matasan Kenya zuwa mutane na gari.

 

Sauti da bidiyo akan labarin