Nasarar raba tagwaye a Afghanistan | Labarai | DW | 06.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nasarar raba tagwaye a Afghanistan

Yaran dai 'yan mata an haifesu ne a gida a lardin Badakhshan bayan ganinsu a hade aka garzaya da su wani asibiti mafi kusa.

Iran Siamesische Zwillinge

Yaran da aka haifa a hade

Likitoci a birnin Kabul na kasar Afghanistan sun sami nasarar raba wasu 'yan tagwaye mata biyu da ke da kwanaki 15 a duniya, aikin raba jariaran da ke zama na farko a Afghanistan karkashin ayyukan wata kungiyar taimakon lafiya ta Charity Hope.

Likitoci biyar ne dai suka shiga aikin fidar da ya kwashe sa'oi biyar ana yinsa a ranar Asabar da ta gabata inda aka raba Ayesha da Sidiqa, wadanda jikinsu ke hada tun daga ciki zuwa kwibi, kamar yadda sanarwar kungiyar da ta yi wannan aiki ta nunar.

Yaran dai an haifesu ne a gida a lardin Badakhshan bayan ganinsu a hade aka garzaya da su wani asibiti mafi kusa, daga nan ne aka kaisu cibiyar lafiya ta Faransa wacce kungiyar agajin ta Chain and Hope ke daukar nauyin ayyukanta.

A cewar kungiyar wannan babar nasara ce ga asibitin a fafutikarsa wajen kula da lafiyar al'ummar kasar Afghanistan.