1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nasarar kafa gwamnatin hadakar Jamus

Ramatu Garba Baba
March 8, 2018

Kwalliya ta biya kudin sabulu a siyasar Jamus bayan da jam'iyyun siyasa suka amince da kafa gwamnati hadaka inda Shugabar gwamnati Angela Merkel za ta samu sabon wa'adi na mulki.

https://p.dw.com/p/2tyXX
Deutschland | SPD-Basis stimmt für GroKo |  Pressekonferenz im Willy-Brandt-Haus
Hoto: Getty Images/AFP/J. MacDougall

Ana ci gaba da samun martani mabanbanta game da matakin samun matsaya na kafa gwamnatin hadaka, watanni bayan zaben kasa baki daya da ya gudana. Jam'iyyun siyasa na kasar ta Jamus wadanda ke cikin majalisar dokoki na sahun gaba wajen mayar da martani kan kafa gwamnati hadakar da mambobin jam'iyyar SPD suka kada kuri'ar amincewa domin shiga gwamnatin tare da CDU/CSU da Shugabar gwamnati Angela Merkel ke jagoranci.