Nasarar dakile cutar Ebola a Kwango | Labarai | DW | 15.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nasarar dakile cutar Ebola a Kwango

Mahukunta a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango sun tabbatar da cewa babu cutar Ebola a kasar.

Ministan lafiya na kasar Felix Kabange Numbi ne ya ba da wannan tabbacin inda ya ce a yanzu babu kwayar cutar kwata-kwata a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango. A watan Agustan da ya gabata ne dai kwayar cutar Ebola ta bulla a kasar da ke yankin Tsakiyar Afirka, inda ta lakume rayuka 49. Sai dai jami'an kiwon lafiya sun bayyana cewa Ebolan da ta bulla a Kwango na da ban-banci da kwayar Ebolan da ta bulla a yankin yammacin Afirka wadda kawo yanzu ta yi sanadiyyar rayukan mutane 5,100 a wannan yanki.