Napolitano ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasar Italiya
April 20, 2013A Kasar Italiya an zabi Giorgio Napolitano a matsayin shugaban kasa, wannan ya biyo bayan ya mika takardarsa ta sake takaran shugabancin kasar, bayan gaggan 'yan siyasan kasar sun nemi ya yi haka, domin kawo karshen takun saka kan zaben sabon shugaban da majalisa za ta yi.
Majalisar dokokin kasar ta kwashe kwanaki uku ba tare da iya zaben sabon shugaban ba. Daga cikin wadanda suka shiga takara sun hada da Franco Marini tsohon shugaban kwadago, da Romano Prodi tsohon babban jami'in Hukumar Tarayyar Turai, duk sun janye takaran da su ke yi na neman shugabancin, gabanin fidda sakamako.
Watanni biyu bayan zaben kasa baki daya 'yan siyasa sun kasa cimma matasayan kafa gwamnati a kasar ta Italiya.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Halima Balaraba Abbas