Namibiya: Diyya muke bukata ba tallafi ba | Labarai | DW | 29.05.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Namibiya: Diyya muke bukata ba tallafi ba

Wasu 'yan Namibia sun bukaci Jamus ta biya diyya ga iyalan mutanen da aka hallaka a zamanin da ta yi wa kasar mulkin mallaka maimakon tallafin raya kasa da ta yi alkawarin bayarwa.

Hukumomi a Namibiya sun bayyana farin cikinsu dangane da abin da gwamnatin Jamus ta yi na amince wa da kuskuren da ta yi na kisan kare dangi a kan kabilun Herero da Nama a zamanin mulkin mallaka. 

Jamus dai ta yi mulkin mallaka a yankin da yanzu ya kunshi kasar Namibiya, inda Jamus din ta bayyana kudurinta na bayar da gudunmawar Euro biliyan daya da miliyan dari uku don ayyukan raya kasa a Namibiya a maimakon diyya.

Sai dai wasu 'yan Namibia mazauna Jamus sun bukaci gwamnatin ta Jamus ta biya diyya ga iyalan mutanen da aka hallaka a zamanin mulkin mallaka maimakon gudunmawar raya kasa da za ta bayar.

Batun tallafin dai ya zo ne sakamakon wata zanga-zanga da ta barke a kasashen biyu na Jamus da Namibiyar kan bukatar biyan diyyar wadanda Jamus din ta hallaka da kuma daukar nauyin wasu manyan ayyukan cigaba a kasar da aka yi wa mulkin mallaka a maimakon ban hakuri kawai.