Nakiya ta tashi a arewacin Mali | Labarai | DW | 30.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nakiya ta tashi a arewacin Mali

Mutane uku suka mutu kana wasu 28 jikkata a sakamakon tashin nakiyar a kusa da garin Gao.

Rahotanni daga Mali na cewar nakiyar ta tashi a sa'ilin da wata motar da ke ɗauke fasinja ke wucewa a kusa da garin Gao. Motar da ke ɗauke da fasinja na kan hanyar zuwa wani taron baje koli na mako da ake yi a kusa da garin na Gao.

Yazuwa yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin, sai dai ana kyautata zaton cewar harin ba ya rasa nasaba da haren-haren da ƙungiyoyin masu jihadi suka saba kai wa a yankin.