Nakiya ta hallaka sojoji a Nijar | Labarai | DW | 14.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nakiya ta hallaka sojoji a Nijar

A Jamhuriyar Nijar sojoji hudu sun hallaka sakamakon taka wani abin fashewa da motarsu ta yi a yankin Diffa da ke fama da hare-haren mayakan Boko Haram.

Wata majiya daga sojan kasar Nijar ta tabbatar da faruwar hatsarin a tsakanin garuruwan Toumour da Bosso da ke makwaftaka da Najeriya tun a ranar Asabar, to amma sai dai ba a samu cikakken labarin faruwar lamarin ba saboda shagulgulan babbar Sallah.

Sojojin kawancen kasashen Nijar Najeriya, Chadi da Kamaru, na ci gaba da kara matsin lamba a yaki da kungiyar Boko Haram a yankin tabkin Chadi yankin da kungiyar ke samun malaba.

Sojojin hudu na Nijar sun gamu da ajalinsu ne sakamakon taka wani abin fashewa da motarsu ta yi a yankin Diffa da ke fama da hare-haren mayakan Boko Haram.