Najeriya:Sabbin alkaluma na hare-hare a garin Rann | Labarai | DW | 21.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya:Sabbin alkaluma na hare-hare a garin Rann

Mutane akalla 236 suka mutu a sakamakon hare-haren da jiragen yakin Najeriya suka kai bisa kuskure.

An kara samu bayanai na sabbin alkalluma na mutanen da suka rasa rayukansu a hare-haren da jiragen sama na yaki na rundunar sojojin Najeriya  suka kai a makon jiya a garin Rann da ke a yankin arewa maso gabashin Najeriyar cikin Jihar Maiduguri bisa kuskure.Shugaban karamar hukumar Kala Balge inda aka kai harin Babagana Malarima ya ce mutane 236 suka mutu.Bayan da jiragen sama na yaki suka jefa bama-bamai biyu daya a kusa da wata rijiyar da ake gina wa 'yan gudun hijira,daya kuma a cikin wata unguwar da ke cike da jama'a makil.