1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya:An sace mutane 14 a Zamfara

May 9, 2018

Daga cikin wadanda ke hannun 'yan bindigar sun hada da wata amarya da ba ta dade da tarewa gidan angonta, kuma yanzu haka 'yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike domin kubtar da mutanen.

https://p.dw.com/p/2xR5C
Polizei in Kano Nigeria
Hoto: Imago/Zuma Press

Yanzu haka mutane 14 ke hannun masu yin garkuwa da mutane a jihar Zamfara inda suke neman kudin fansa, wadannan mutane dai an kamasu ne kan hanyarsu ta zuwa kasuwa, lamarin da al'ummar Jihar ta Zamfara ke bayyana ko in kula na mahukunta. Hakan dai na ci gaba da sanya fargaba a zukatan mutanen garin musamman mazauna yankunan karkara. Lamarin na yin garkuwa da mutanen ya zamar ma masu garkuwar wata sana'a ta yau da kullun inda in sun sako wasu bayan sun amshi kudin fansa sai kuma su kama wasu. A baya dai maharan sun saci dabbobi da dama a Jihar ta Zamfara inda yanzu wasu daga cikin mutanen yankunan ke cewar dabobin sun kare shi ya sa suka koma satar mutane don neman kudin fansa. Jihar Zamfara dai na ci gaba da fuskantar hare-hare 'yan bindiga masu kashe mutane gami da yin garkuwa da su.