1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Zargin gwamnatocin jihohi da gazawa

December 3, 2022

Kasa da watanni shida da kaiwa ya zuwa karshen wa'adin mulkin jam'iyyar APC a Najeriya, daga dukkan alamu an fara nunin yatsa a bangare na gwamnatin tarrayar kasar da ke zargin jihohi da gazawa.

https://p.dw.com/p/4KPjM
Hoto: Koula Sulaimon/AFP

Tun daga tsakiyar wannan mako ne dai aka fara hango alamun raba gari a tsakanin gwamnatin tarrayar Najeriya da na jihohin kasar kan ko wane ne mai laifi bisa matsi na tattali na arzikin da kasar ke fuskanta.

An faro ne da wani minista na gwamnatin na zargin karkatar da kudaden da suke samu daga ayyukan rage fatara da talauci a tsakanin al'umma, ya zuwa ga kwangilolin da ba su da tasiri a rayuwa ta 'yan kasar.

Kafin daga baya shi kansa shugaban kasar ya fito fili wajen zargin gwamnonin da wasoso da kudade na kananan hukumomin da ake yiwa kallon sun taimaka wajen ta'azzara talaucin da kasar ke wafuskanta yanzu.

Karin bayani: Najeriya za ta kashe Naira tiriliyan 20 a 2023

Shi kansa mashawarci na tsaron kasar dai ya zargi gwamnonin da hayar masu ta'adda, kafin wata sabuwar sanar da safiyar ranar Jumma'a da ke lissafin dalla-dallar abin da gwamnatin tarrayar ta baiwa jihohin yankin Niger Delta da ke da arzikin man fetur.

Niger Delta | Muhalli
Niger Delta mai arzikin man fetur na daga cikin yankunan Najeriya da ake zargin mahukunta da yin sama da fadi da kudaden raya yankinHoto: Friedrich Stark/imago

Shugaba Muhammadu Buhari dai alal ga missali bai boye yadda gwamnonin ke watsi da batun doka wajen aikata cin hancin da ke mayar da kasar zuwa can baya ba.

"Yadda ake yiwa kananan hukumomin, abin da suke yi shi ne, wannan abin da na sani ne. Kudin da ke zuwa daga gwamnatin tarraya zuwa jihohi, mu dauka Naira miliyan 100 ne, miliyan 50 za a tura su ne ga shugabannin kananan hukuma tare da takardar cewar ya karbi Naira miliyan 100. Gwamna zai sa ragowar a aljihu tare da rabawa wadanda ya ga dama. Sannan kuma shi shugaban karamar hukumar zai ga nawa ne ya zama tilas ya biya a matsayin albashi, ragowar aiyyukan raya kasa kuma ko oho. Kudin albashi zai biya, ragowar kuma zai saka cikin aljihunsa. Najeriyar tamu ke nan. Abu ne maras kyau, kuma me yin sa ba jahili ba ne. Kila ma lauya ne, kwararre, amma kuma yana aikata irin wannan cin hanci."

Karin bayani:Najeriya: Bashi ya kai wa mahukunta wuya

To sai dai kuma in har gwamnoni sun yi kunnen kashi da batun doka, ana kallon jerin zargin da alamun raba gari a tsakanin tsofaffi na abokan takun da ke shirin karewa tare da kowa amsa suna na mahaifinsa.

Sabon rikicin dai a fadar Dr Umar Ardo da ke takara ta mukamin gwamnan jihar Adamawa a karkashin inuwar jam'iyyar SDP na nuna "alamun raba hanya a tsakanin tsofaffi na abokan burmun guda biyu".

Kokari na Abujar na tabbatar da 'yanci na kananan hukumomin a karkashin wani umarni na shugaban kasar dai ya kare ba tare da kaiwa ya zuwa cika buri ba.

Gwamnonin ne dai ake ta zargi da ingiza majalisu na jihohi wajen kau da kai bisa ga bukatar neman 'yanci na kanana na hukumomi na kasar.

To sai dai kuma duk da jeri na matakan kuma a fadar Auwal Mu'azu da ke sharhi kan harkokin mulki da siyasa, da kamar wuya "iya kaiwa ga karkatar da duk wani laifi ga bangare guda na mulki na kasar a cikin rushewa ta tattalin arzikin tarrayar ta Najeriya".