Najeriya: Zanga-zanga kan karin kudin wutar lantarki | Siyasa | DW | 08.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Zanga-zanga kan karin kudin wutar lantarki

'Yan kwadago sun gudanar da zanga-zanga a sassa daban-daban na Tarayyar Najeriya don nuna adawarsu da karin kudin hasken wutar lantarki da hukumomi suka yi.

Dubban 'yan kwadago na Tarrayar ta Najeriya dai ne suka fantsama kan titunan kasar inda suka yi ta rera kalamai na nuna rashin amincewarsu da wannan karin wanda ya kai kaso 45 cikin 100 na tsohon farashin da 'yan kasar ke biya can baya. Masu boren dai sun ziyarci hukumar samar da hasken wutar lantarkin da majalisar dokokin kasar inda suka ce ba za su amince da sabon karin ba.

Karkashin jagorancin manyan kungiyoyin kwadagon kasar biyu wato NLC da TUC suka jagoranci tattakin da aka yi wanda ya samu halartar wasu kungiyoyi na fararen hula. Comrade Ayuba Waba da ke zaman shugaban kungiyar kwadagon kasar ta NLC ya ce karin zai kara hali na matsi da talaka ke ciki musamman ma dai da ya ke kasar na fama da kalubale iri-iri.

Nigeria Arbeiterkongress protestiert 2010

'Yan kwadago sun ce karin wutar lantarki zai jefa talaka cikin matsanancin hali

Baya ga Abuja, a wasu sassan Najeriya din dai, an gudanar da wannan zanga-zanga. A jihar Sokoto da ke yankin arewa maso yammacin kasar ga misali an yi wannan bore inda masu amfani da wutar lantarki a jihar suka dafawa 'yan kwadagon wajen nuna rashin amincewarsu da wannan kari wanda suka ce zai sake jefa al'umma ne cikin mawuyacin hali.

To sai dai yayin da 'yan kwadago da sauran jama'ar gari ke nuna tirjiya ga wannan kari, masu ruwa da tsaki a kan samarwa da ma rarraba hasken wutar lantarkin sun ce karin ya zame musu dole ne saboda kokarin da suke yi na ganin lamura sun daidaita, ta yadda za a iya samar da wutar ta lantarki isasshiya ga al'ummar ta Najeriya.

Sauti da bidiyo akan labarin