Najeriya za ta yaƙi Boko Haram | Labarai | DW | 30.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya za ta yaƙi Boko Haram

Shugaban Nigeriya Goodluck Jonathan ya sha alwashin ƙaddamar da yaƙi tukuru ga Ƙungiyar Boko Haram.

Shugaban ya bayyana haka ne a jiya a jawabin da yayi a lokacin da ake gudanar da bukukuwan zagayowar cikar shekaru 15, da ƙasar ta sake komawa bin tubar ta demokraɗiyya bayan tsaikon da aka samu na juyin mulkin sojoji. Shugaban ya umarci sojojin ƙasar da su ƙaddamar da yaƙin a kan ƙungiyar sannan ya ƙara da cewar.

''A shirye na ke na kare demokraɗiayyarmu da haɗin kan ƙasa, domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a harkokin siyasa ta hanyar yin yaƙi da Boko Haram.''

Tun a shekarun 2009 aka fara samun tashe-tashen hankula na Ƙungiyar ta Boko Haram a arewacin Najeriyar, wanda a cikinsa sama da mutane dubu biyu suka mutu tun farkon wannan shekara.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe