Najeriya za ta rage cunkoso a gidajen yari | Siyasa | DW | 19.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya za ta rage cunkoso a gidajen yari

Gwamnatin Najeriya na ci gaba da fuskantar kalubale a kokarin aiwatar da shirin yi wa gidajen yari garambawul a yayin da jama'a da kungiyoyi masu fafutuka ke cewa ana aikata laifuka da suke tauye hakkin dan adam.

Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamnati Najeriyan ta soma mayar da martani a game da kame tsohon ministan shari’ar kasar, Bello Adoke da rundunar 'yan sandan kasa da kasa ta Interpol ta yi a Dubai. Kafin ya tafi Dubai, Ministan  shari’ar, ya baiyana cewa matakan da suka fara dauka na gyara hukumar kula da gidajen yari ta koma wuraren gyara halayen jama’a ta fara samun nasarori dama yi wa fursunoni afuwa.

Sauya suna bisa doka da aka yi wa hukumar kula da gidajen yari Najeriya da ta koma hukuma mai gyara halayen jama’a tun bayan da shugaban Najeriyar Muhammadu Biuhari ya rattaba hannu a kan dokar, ya sanya jefa fata ta samun sauyi, to sai dai shiru da aka ji daga mahukunta tun bayan daukar wannan mataki da ya sanya koken sauyin na neman zaman a sauya suna kawai, ya sanya duba lamarin. 

Kokari na rage cinkoso a gidajen yarin Najeriyar dai babban batu ne a wannan aiki, abin da ya kai ga kafa kwamiti na musamman da ya duba halin da gidajen yarin ke ciki bisa bukatar daukan mataki na yi masa garambawul, musamman biyo bayan zargi na taken hakin jama. Sakamakon bullo da wadannan sauye-sauye da koya wa fursunonin sana’oi maimakon ci gaba da tsaresu kawai.

A yayin da ake samun wadanan sauye-sauye, har yanzu akwai sauran aiki a fannin kyautata tsarin hukumar kula da gyara halayen jama’a a kasar duk da bullo da na'urar daga ofishin ministan shari'a ya ke duba masu laifin da ya kamata a kai su kotu, domin kasha casa'in na fursunonin da ake tsare dasu, suna jiran a yi masu shari’a ne.

Sauti da bidiyo akan labarin