Najeriya za ta farfado da kamfanin kera makamai | Labarai | DW | 07.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya za ta farfado da kamfanin kera makamai

Shugaban Najeriya ya bada umarnin farfado da ma'aikatar kera makamman kasar domin magance matsalolin dogoro ga kasashen waje.

Shugaban kasar Muhamadu Buhari ya bada umarni ga ofishin ministan tsaron kasar kan wannan batu na ganin an farfado da kamfanin na kera makammai da suka dace da zamani domin magance wasu bukatun sojojin kasar, inda ya ce dogaron da Najeriya ke yi da kasashen waje kan batun na makammai da wasu kayyakin soja, abu ne na takaici da baza'a yarda da shi ba nan gaba.

Dama dai a shekarar 1964 Najeriya ta kaddamar da kamfanin kera makamman na DICON mai cibiya a birnin Kaduna da ke Arewacin kasar, amma kuma aka dakatar da ayyukansa, inda yanzu kamfanin ya koma ga kere-keran kayyakin da ba na soja ba.