Najeriya za ta fara cinikin zinare
July 16, 2020Talla
A yayin da ya kaddamar da shirin na cinikin zinare a fadar gwamnatin kasar a wannan Alhamis a birnin Abuja, shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yana san ran samar da ayyukan yi ga sama da mutum dubu 250 a karkashin wannan shiri.
An kuma kaddamar da shirin ne tare da cinikin wani danyen zinare daya kai kilo 12.5 da masu hakar zinarin na jihar Kebbi suka kai ga hakowa sannan kuma babban bankin kasar na CBN ya biya dalar Amirka dubu 800 kansa.
Karkashin wannan shirin shugaba Buhari ya ce za a ba da lasisin hakar danyan gwal din, wanda ya ce babu shi a baya da kuma ake tunanin yana daga cikin hummun habaisin tashin hankula a shiyoyin Arewa maso yammacin kasar.