1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kungiyar Cislac za ta yaki cin hanci

November 9, 2018

Kungiyar farar hular nan ta Cislac tare da hadin guiwar hukumomin yaki da cin hanci sun kafa cibiya da za a iya kai koke gabanta kan cin hanci da rashawa da take hakkin jama’a.

https://p.dw.com/p/37yFS
Nigeria Symbolbild Korruption
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Wannan cibiya dai ita ce irinta ta farko da aka samar a Najeriya wanda  kungiyar ta Cislac mai yakar mumunar dabi'a ta cin hanci da rashawa da hadin guiwar sauran hukumomin da ke wannan aiki a kasar suka yi, an tsara ta ne ta hanyar kare dukkanin masu kai bayanai da ke taimakawa wajen bankado masu rub da ciki a kan dukiyar gwamnati. Wannan ya biyo bayan matsalolin da aka fuskanta ga masu tonon silili, inda duk da ladar kudi da ake basu in tarko ya kama suke fuskantar barazana.

Akwai dai jami'an hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na Najeriyar da suke wakilai a wannan cibiya da aka saukaka hanyar aikewa da bayanai ta sakon email da ma waya. An gano rashin samun jama'a da ke son yin fallasa kan wadanda ake zargi da cin hanci dama take hakokin jama'a har da  fyade saboda tsoron bita da kuli da ake ganin ya haifar da koma-baya sosai.

Kwararu na bayyana cewa saukaka hanyar tonon siili da samar da kariya zai taimaka ainun wajen karfafa yaki da cin hanci da rashawa da sannu a hankali masu wannan dabi'a ke kara fadawa tarkon yaki da ita a Najeriyar.