Najeriya: Takaddamar gyaran kundin tsarin mulki | Siyasa | DW | 13.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Takaddamar gyaran kundin tsarin mulki

Majalisar datawan Najeriya ta gaza yin gaban kanta a kan umurnin kotun koli da ya hana ta cigaba da gyaran fuska ga tsarin mulkin kasar inda ta ce yanzu kan za ta ruga kotu.

Fiye da sa'o'i uku ‘yan majalisar datawan suka kwashe suna tattaunawa a asirce a kan wannan batu a tsakanin wadanda ke ganin suna da huja ta tsarin mulki su yi gaban kansu, da wadanda ke kashedi da yin hakan bisa ga umurnin kotun kolin da ke wa lakabi daga hukuncinki sai dai a dangana.

Daukar matakin ya nuna dakatar da yunkurin da suka yi duk da dagewar da majalisar ta yi da farko kan cewa babu wata doka da za ta iya hanata gudanar da aikinta na kafa dokoki ya sanya tambayar shin me suka hango ne ya sa suka sauya matsayin nasu? Santa Ibrahim Musa da ke zaman guda daga cikin 'yan majalisar ya ce "an kawo shawarwari cewa a tsaya a bi doka don mu masu yin doka "

Ana dai yi wa ‘yan majalisar kallon masu yawan kurari da cika baki a kan abinda ya shafi yin gaban kansu a kan shugaban Najeriyar, duk kuwa da cewa doka ta basu ikon yin haka a kan abubuwan da ba su kaima ga kotun kolin ba amma sun kasa yin hakan. Anya ba tsoro suka ji ba ya sanya su ja baya a kan batun? Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya ce "ai babu tsoro a kan wannan magana shi yasa da ka ke tambayata ma ai murmushi na ke yi".

Sassan da shugaban ke da ja a kansu a kan yi masu gyaran fuska dai sun hada da batun karbe ikon sanya hannu a kuduri kafin ya zama doka daga hannun shugaban kasar, da rarrabe ofishin babban mai shari'a na kasa da na babban mai adana kudi.

Duk da ikon da majalisun datawa da na wakilai ke da shi na amincewa da kuduri ba kasafai suke amfani da wannan iko ba, abinda ya sanya jama'a da dama yi masu kalon ‘yan amshi shatar ga gwamnati. Da alamun dai aikin sake fasalin tsarin mulkin Najeriyar ya kama hanyar zama na babar giwa duk da kwashe fiye da shekaru uku da ma kudi sama da Naira bilyan guda da aka kashe a kansa, abinda zai sake mayar da aikin danye ga majalisa ta takwas da ke shhirin kama aiki.

Sauti da bidiyo akan labarin