1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta umarci sojoji su koma bariki

Ibrahima Yakubu/USUJune 23, 2015

Aksarin 'yan Najeriya sun yi marhaba da umartan sojoji su kawar da shingaye kan tituna a fadin kasar bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da hakan

https://p.dw.com/p/1FmFN
Nigeria Maiduguri Militär Sicherheit Anti Boko Haram 2014
Hoto: picture-alliance/epa

Wannan batun dai ya janyo maida martani daga bangarorin al'umman kasar daban-daban, gami da umarnin da sabon zababben shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bada. Inda suka nuna matukar murna da zuwan wannan rana, domin kowa suka ce sun fara samun chanjin da ake bukata, to sai dai wasu na ganin cewa, lallai dai kam akwai bukatar yin taka tsantsan, domin kaucewa karuwar ayyukan 'yan fashi da makamai da wasu masu neman tayar da zaune tsaye.

Bada umarnin ruguza dukkanin shingayen tsaron Najeriya ya sanya masu safarar kayan gwari da masu fataucin dabbobi da direbobin manyar motoci, fitowa ta kafafen watsa labarai suna nuna murnan su a fili, gami da yunkuri da sabuwar gwamnatin kasar ta aiwatar. Honorable Mohammad Ali tshohon dan majalisar dokokin jihar Kaduna, ya dade yana nuna adawarsa da sukar kakkafa wadannan shingayen binciken ababen hawan, bisa la'akari da yadda suka zamo wata matattara tauye hakkin jama'a da walakanta masu tura babura.

Sai dai ita kuwa Helin Musa daya daga cikin 'yan kungiyoyin dake fafatukar kare 'yancin mata a jihohin arewa Najeriya, ta yi korafi kan umarnin gwamnatin Nigeria kan rugurguza wadannan shingayen tsaro tana mai cewa "ban ji dadin cire wannan shingayen tsaro ba, domin yin hakan zai haifar da matsalolin karuwar rashin zaman lafiya da sace-sace da wasu ayyukan da suka jibanci na 'yan ta'adda. Sai kuma Helin Musa ta gargadi dukkanin masu karban na goro daga wuraren jama'a da su daina yin haka, domin ya taka dokokin kasar"

Nigeria , Jos , Checkpoints gegen Boko Haram helfen
Hoto: DW/Katrin Gänsler