Najeriya ta tsaurara tsaro a tsakanin Abuja da Kaduna | BATUTUWA | DW | 30.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya ta tsaurara tsaro a tsakanin Abuja da Kaduna

Rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna ta kara yawan jami'an tsaro a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna domin murkushe masu satar mutane biyo bayan nasarar ceto dalibai uku da aka yi daga masu garkuwa da mutane. 

A wata takardar sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna Yakubu Sabo ya rarraba wa manema labarai, ya bayyana cewa zaratan 'yan sanda na (IRT) da wasu zaratan da ke aikin gano masu garkuwa da mutane sun ceto daliban jami’ar Ahmadu Bello Zaria guda 3, da aka yi garkuwa da su a titin Kaduna-Abuja da ma sauran wasu matafiya, Yakubu yace mun sami damar kama mutane guda 6, kuma daga cikinsu akwai daliban jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria da kuma sauran wasu mutane da masu sata da garkuwa da mutane ke tsaye da su a cikin dajin Kaduna. Sabo yace bayan samun labarin aikata wannan mummunar aiki da masu garkuwan suka yi ne, sai ‘yan sanda suka fantsama cikin dajin domin kamo wadannan bata-gari. 

A cewar kakakin rundunar Yakubu Sabo, an sami saukin ayyukan masu garkuwa da mutane a kan hanyar na tsahon watanni biyu kamin afkuwar abun da ya faru na mako daya, da masu satar mutanen suka sake dawowa kan wannan hanyar. Ya ce ina mai tabbatar maka da cewa mun kara yawan jami’an tsaro don duba wannan hanayar, kuma nan gaban kadan ba da jima wa ba ne za a magance wannan matsalar ta sace-sacen al'uma da kuma garkuwa da su. Sabo, ya nunar da cewa, wadannan masu garkuwar sun bude wa motar fasinja wuta ne, suna sanye da kayan sojoji don batar da kama, kuma ya ce har yanzu jami’ai na can cikin daji suna farautar masu garkuwar. 

Duk da cewa dai gwamnatin jihar Kaduna ta kara yawan jami’an tsaro a kan hanyar, to sai dai yawancin direbobi da sauran matafiya da ke bin hanyar na kasancewa cikin dar-dar, kamar dai yadda shugaban kungiyar masu Taxi na haya a Kaduna Mr Jerry Sheyin, ke cewa. Ya ce dukkanin direbobinmu da ke bin wadannan hanyoyin na zama cikin dari-dari da fargabar rashin sanin mai zai iya faruwa a duk lokacin da suka dauki hanyar Kaduna zuwa Abuja.

A cewar kwararrun masana a harkar tsaro a Najeriya, ya zamo wajibi gwamnati ta tashi tsaye wajen kawo karshen ayyukan ma su fashi da makami da satar jama’a, ita kuwa dai gwamnatin tarayyar Najeriya, bayyana wa ta yi cewa a cikin watanni bakwan da suka shude ‘yan bindiga sun kai hare-hare har sau 330, tare da kashe adadin mutane 1,400 daga Janairu zuwa Yuli.

Sauti da bidiyo akan labarin