Najeriya ta kauce wa yin kullen corona don kare tattalin arzikinta | Siyasa | DW | 21.12.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya ta kauce wa yin kullen corona don kare tattalin arzikinta

A yayin da miliyoyin al'ummar Najeriya suka fara jin radadin zagaye na biyu na annobar Covid-19, kasar na fuskantar rudani a tsakanin kare lafiyar 'yan kasar da kuma tabbatar da abincin da lafiyar ke da bukata.

Can a zagayen farko dai tarrayar Najeriyar ta zabi batu na fifita lafiyar al'umma bisa batu na tattali na arzikin kasar kan hanyar neman yakar annobar Covid-19.

Mahukunta na kasar dai sun yi nasarar kulle daukacin tarrayar Najeriyar na tsawon wata da watanni da nufin rage radadin annobar a tsakanin al'umma.

Karin bayani: Najeriya: Karya ka'idojin yaki da corona

To sai dai kuma zabin ya zamo mai tsada a tsakanin talakawan da suka fuskanci karuwar talauci mai zafi da kuma mahukuntan da suka sha da gumin goshi a yunkurin tawayen mabiya.

Daukar zafin jikin matafiya lokacin da suke isa filin jirgin sama na Legas a Najeriya

Daukar zafin jikin matafiya lokacin da suke isa filin jirgin sama na Legas a Najeriya

Ana dai ta'allaka ita kanta masassara ta tattali na arzikin da kasar ke ciki a halin yanzu da matakan kullen da ya tsayar da daukaci na kasuwancin al'umma ko bayan rashin kudin man fetur da kasar ke dogaro da shi.

Najeriyar dai ta fada zagaye na biyu na annobar tare da fuskantar karuwar ta'azarar annobar da ma kisan al'umma a ko'ina cikin kasar a halin yanzu.

Karin bayani:Corona: Najeriya ta bude asusun Naira bilyan 500

To sai dai kuma maimakon komawa gidan jiya dai jihohi dabam-dabam a cikin kasar na daukar matakai mabambanta da nufin tunkarar sabo na zagayen annobar.

Kuma kama daga Legas in da gwamnatin jihar ta kakaba tarar Naira 20,000 kan wadanda suka yi fatali da ka'idojin ya zuwa a Kaduna da jihar Imo in da ma'aikata ke shirin komawa aiki a gida dai kusan daukacin jihohi na kasar sun manta da batun kulle da ke zaman salo a zagayen can baya.

Abuja lokacin matakan kulle a zagayen farko na corona

Abuja lokacin matakan kulle a zagayen farko na corona

Da'ami bisa a lafiya ko kuma kokari na jefa kasa cikin barazana mai girma dai sama da mutane dubu biyar ne suka kamu da annobar a cikin makon da ya shude kuma mafi zafi tun bayan bullar anobbar a watan Fabrairun da ya shude. Kuma a fadar Dr. Ado Muhammad da ke zaman kwararre a harkar ta lafiyar al'umma, mafita ga 'yan kasar da ke neman kaucewa kullen dai na zaman bin dokoki na hukumomi a matakai dabam-dabam cikin kasar.

Karin bayani: Najeriya: Cece-kuce a yaki da coronavirus

A ranar Talata ake sa ran babban taro na kwamitin gwamnatin kasar game da corona, kwamitin kuma da ke nazarin mafita ga kasar da ke kokarin kauce wa ta'azarar annobar amma kuma ke tsoron sake jefa 'yan kasar cikin halin kulle.

Sauti da bidiyo akan labarin