Najeriya ta fara samun habakar tattalin arziki | Siyasa | DW | 10.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya ta fara samun habakar tattalin arziki

Bayan share tsawon lokaci ana cikin duhu gwamnatin Najeriya ta ce an fara ganin haske wajen bunkasar tattalin arzikin kasar wanda zai kara habaka zuwa shekara badi musammun ma a kan harkokin noma.

Tun a farkon fari dai hukumar lamuni ta duniya ta fitar da hasashen da ke fadin da akwai sauran tafiya a tsakanin Najeriya da kokari na ficewa a cikin halin masassara ta tattalin arziki. To sai dai kuma ta fara nuna alamun sauyi tare da wani sabon rahoton hukumar da ya ce tattalin arzikin na shirin kara ganin haske a shekarar badi. Tun daga zango na uku na shekarar bana dai a fadar rahoton na IMF da ya yi nazarin tattalin arzikin ya ce Najeriyar za ta kai ga ficewa a cikin halin koma baya na tattali  arzikin da ta fada baya.

Ana dai kallon sauyi na tattalin arzikin na da ruwa da tsaki da zaman  lafiyar da aka samu a Niger Delta da ya yi nasarar samar da  yawan man kasar zuwa ganga miliyan biyu da doriya, a kullum tare da mayar da hankali ga harkar noma da ma'adinai cikin kasar.

 

Sauti da bidiyo akan labarin