Najeriya ta fara jigilar ′yan kasarta daga Bangui | Siyasa | DW | 03.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya ta fara jigilar 'yan kasarta daga Bangui

Jiragen sama biyu ne dai suke dauke da 'yan Najeriya su kimanin 360 mafi yawansu mata, yara kanana da kuma tsofafi.

Zangon farko na ‘yan Najeriya da suka samu tsira daga yakin da ake kafsawa a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya suna cikin jirgi kan hanyarsu ta zuwa Najeriya, bayan da hukumar kai daukin gaggawa ta NEMA ta samu nasarar kwaso su daga Bangui hedikwatar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, a yanayi juyayin mumunan halin da suka samu kanssu a ciki.

Jiragen sama biyu ne dai suke dauke da 'yan Najeriya su kimanin 360 mafi yawansu mata, yara kanana da kuma tsofafi, a zangon farko na 'yan Najeriyar da aka fara aikin kwasosu daga Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, bayan mumunan halin da suka samun kasu a kasar, domin kiuwa a fuskokinsu ma sun bayyana hakan. Koda a fuskokinsu sun bayyana hakan.

A zahiri yake cewa sun gamu da tasku domin kuwa sun samu kasansu a tsakanin rayuwa da mutuwa, saboda rustawara day akin da ake kafasawa a Jamhuriyar Afrika ta tsakiyar day a kasance na addini tsakanin musulmi da Krista day a rutsa das u, domin bayan sun samu mafaka a ofishin jakadancin Najeriya da ke birnin Bangui, a can din ma wata sabuwar matsala suka shiga da ta yi kama da gaba kura baya damisa.

Na tambayi Aishi Imam daya daga cikin 'yan Najeriya da ke can wacce ta tabbatar man cewa mutanen sun shiga cikin jirgin kuma suna kan hanyar dawowa Najeriya.

"E, Najeriya ta turo jirgi guda biyu gamu nan maganar da nike yi maka muna a filin jirgi mutane sun shiga cikin jirgi an rufe ma kofar jirgi, amma an samu wata yara matsala ne tsakanin ma'aikatan filin jirgi, amma ina ganin za a sasanta."

Muhammad Sani Sidi

Alhaji Sani Sidi shugaban hukumar NEMA

To sai dai jinkirin da aka dade an samu ya haifar da zargi ga gwamnatin Najeriya na gazawa, amma Alhaji Sani Sidi shi ne shugaban hukumar kai daukin gaggawa ta Najeriya ya bayyana abinda ya haifar da jinkirin kwaso 'yan Najeriyar.

"Wannan hasashe da ake yi bah aka yake ba, domin ana kokarin a tabbatar da cewa wadannan mutanen da ake sonb a dawo das u Najeriya, shin 'yan Najeriya ne ko kuwa a'a, kuma yan Najeriya ne suna da cikakkun takardu ko kuwa a'a, don yawancinsu basu da cikakken takardun tafiya, amma da zarara na tabbatar da suna da takardun za'a dawo das u. Kai har ma wadanda basu da takardu za a dawo da su, don jami'an da suka tafi suna nan suna shirya masu takardu na dawowa."

Tanajin kai su yankunansu a Najeriya

A yanzu da suka iso Najeriya ko akwai wani tanajin da aka yi masu kafin a mikasu ga jihohin da suka fito? Har ila yau ga Alhaji Sani Sidi shugaban hukumar kai daukin gaggawa ta Najeriyar.

A mafi yawan lokuta dai akan zargi gwamnatin Najeriya da jan kafa wajen kai dauko dam ka kwaso yan asalin kasarta da kan samu kansu a mawuyacin hali a yanayi da rigingimu ko yaki a cikin kasar da ma kasashen waje, abinda ke jefa damuwar saboda illar da hakan ked a shi ga ‘yan kasar musamman wajen nuna kishin kasa.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idriss
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin