1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta fada matsalar tattalin arziki

Abdul-raheem HassanSeptember 1, 2016

'Yan Najeriya na fargabar makomar rayuwarsu bayan da hukumar kididdiga bayyana arzikin kasar ya samu koma baya.

https://p.dw.com/p/1JuQe
Karikatur Nigeria Wirtschaft Rezession
Hoto: DW

Alkaluman da hukumar kididdiga a Najeriyar ta saki sun nuna an samu tawayar kaso biyu cikin dari na arzikin kasar da mutanenta, a watanni ukun da suka gabata.

Hakan dai na nuni da cewa, Najeriya ta fada cikin kangin tattalin arzikin da ya fi kowanne a tsawon shekara goma a tarihin kasar. Ko a watanni ukun farko na wannan shekara, tattalin arzikin Najeriyar ya fuskanci tankarda inda aka samu koma baya da kaso 1.70.

Sai dai kuma alkaluman sun nuna cewa komadar ta wannan lokacin ba ta kai ta watanni ukun farko na mulkin shugaba Muhammadu Buhari ba, to sai dai Hukumar ta Kididdiga dai ta ce kasar ta samu tawayar arziki da kaso 2.35 a wannan karo.

Kasar dai wadda ke jerin kasashen da ke kan gaba wajen albarkatun man fetur a nahiyar Afirka, ta dogara ne kacokan bisa kudaden da ake samu daga sayar da man. An dai ganin cewar faduwar farashin man ne a kasuwar duniya ya haddasa wa kasar halin da take ciki.