Najeriya ta bukaci mayar mata da kayan tarihinta da aka sace | Zamantakewa | DW | 30.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Najeriya ta bukaci mayar mata da kayan tarihinta da aka sace

A duk fadin duniya ana baje kolin kayayyakin tarihi da na al'adun gargajiyar kasashen nahiyar Afirka, musamman kayayyakin tagulla al'ummomin birnin Bini na jihar Edon Najeriya da turawan mulkin mallaka suka sace.

Ikhuehi Omonkhua yana yi wa maziyarta maraba a gaban kofar gidan adana kayayyakin tarihi na kasa da ke birnin Bini da aka bude a shekarar 1973, da yanzu aka yi masa cikakken gyara yake da kuma muhimmanci a Najeriya. Dalili shi ne baje kolin wasu kayayyakin tagulla na rayuwar yau da kullum da kuma yanayin yaki a yankin. Daga cikin kayayyakin na tsawon daruruwan shekaru da aka yi wa gyara da na kan wata mata da suka sa yankin birnin na Bini da ke zama shalkwatar jihar Edo ya shahara a duniya baki daya, inji Ikhuehi Omonkhua mai yi wa maziyarta jagora a gidan adana kayan tarihin.

Bronzen in Benin City und deren Rückkehr nach Nigeria (DW/Katrin Gänsler)

Ikhuehi Omonkhua mai yiwa maziyarta kayan tarihi jagora

"An sarrafa tagullar farko a Bini a shekara ta 1288, zamanin Sarki Oba Ogola. An yi aikin ne don tattara bayanai na al'adun tarihi a fadar Sarki. Basarake ne kadai ke da 'yanci na musamman na amfani da tagullar."

Kadan daga cikin wadannan kayayyakin tarihin ne ake yi ganinsu a birnin na Bini, domin akasaraninsu musamman muhammai daga cikinsu an sace lokacin mulkin mallaka, kuma har yau ana bajesu a manyan gidajen adana kayayyakin tarihi na kasashen Turai, kamar a birnin London na Birtaniya da birnin Leipzig a Jamus da birnin Vienna na kasar Ostriya. A jimilce kayayyakin tarihi fiye da dubu uku ne Turawa 'yan kasuwa da wakilan gwamnatin mulkin mallaka ta Birtaniya suka sace daga Bini a shekarar 1897. Yawanci an yi gwanjonsu a Turai.

Theophilus Umogbai da ke alkinta kayayyakin tarihi a gidan adana kayan a Bini ya ce a karon farko ya fara ganin muhimman kayakin tarihin kasarsa a Birtaniya.

"Gaba daya kamar mafarki sai ga kayayyakin tarihinmu. Na ma dauki hotunansu. Abin ya sosa mini rai. A hannu daya na yi farin cikin, sannan a daya hannun kuma na yi bakin ciki, domin suna a wurin da bai dace ba. Tsawon shekaru ana baje kolin wata kaza ta tagulla da ke zama muhimmiyar alama ta sarauniyarmu. Wannan wulakanci ne gare mu."

Burin Umogbai shi ne a mayar da kayan tagullar Najeriya. An dai kai wasu Najeriya har ana baje kolinsu a Bini. Omoruyi Charles daya ne daga cikin mutane kimanin 70 da suka kai ziyarar gane wa ido a gidan tarhin na Bini.

Bronzen in Benin City und deren Rückkehr nach Nigeria (DW/Katrin Gänsler)

Theophilus Umogbai jami'in kula da gidan tarihi na birnin Bini a Najeriya

"A matsayi na dan garin Bini ina bakin cikin yadda mutanen nan suka sace kayayyakinmu na tarihi. Ba na jin ma sun nemi gafara a hukumance. Matakin farko shi ne a fara maido mana da kayanmu."

Tun tsawon shekaru ake tattaunawa tsakanin gidajen adana kayayyakin tarihi na Turai da hukumar kula da gidajen adana kayayyakin tarihi ta Najeriya bisa wannan manufa ta mayar wa Najeriya wadannan kayayyaki. Muhimmin taron da aka yi kan wannan turba shi ne a jami'ar Cambridge a shekarar 2016, inda aka tattauna game da sauran kayayyakin tagullar.

 

 

Sauti da bidiyo akan labarin