1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS: Yunkurin hada kan kasashe

October 23, 2018

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Benin Patrice Talon, sun kaddamar da wani gini da jami'an shige da fice dana hana fasakauri za su rika amfani don tabbatar da doka da oda akan iyakokin kasashen.

https://p.dw.com/p/373B3
Lagos Port Hafen Nigeria
Hoto: AFP/Getty Images

A wannan Talata, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da takwaransa na Benin suka kaddamar da wani gini da jami'an shige da fice da wadanda ke hana fasakauri wato Custom za su rika amfani da shi don tabbatar da doka da oda tsakanin kasar da makociyarta. An dai yi wannan biki a kan iyakar nan ta Seme da ke tsakanin kasashen biyu.

Ginin na zamani ko shakka babu wani makami ne na tabbatar da bin doka da oda ta yadda za a magance matsalar fashi akan iyakokin Najeriya. Shugaba Buhari ya jaddada bukatar da ke akwai na kasancewar Afirka ta zama tsintsiya daya madaurinki daya a dukkan al'amurran yau da kullum na kasashen Afirka baki daya.

Wannan mataki na habaka cinikaiya a tsakanin kasashen baki daya wanda hakan zai rage barazana ta tsaro da kiwon lafiya bisa yadda kan iyakar za ta tafi da sauran kasashena duniya kafada da kafada. Ambasadan kungiyar gamaiyar Turai a Jamhuriyar Benin Mr John Pink ya ce bayan bayar da gudummowa ta gini kungiyar za ta tabbatar ana bin ka'idojin da aka sanya a gaba.