Najeriya: Sojoji za su sake komawa fagen fama | Siyasa | DW | 28.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Sojoji za su sake komawa fagen fama

Gwamnatin Najeriya ta yanke shawarar mai da cibiyar yaki da kungiyar Boko Haram a Maiduguri fadar gwamnatin Jihar Borno domin kawo karshen hare-haren da kungiyar ke kai wa.

Tuni dai da gwamnatin ta umarci manyan hafsoshin tsaro kasa da sama na kasar da su koma yankin da nufin tinkarar annobar da ke iya kai wa ga maida hannun agogo zuwa  baya. Hakan kuwa ya biyo bayan sabbin hare-hare da kungiyar Boko Haram ke kai w a Jihar ta Borno.

Abin kuma da a nan a Abuja ya tilasta kiran wani taron gaggawa na majalisar tsaron kasar da ta zauna ta kuma yanke shawarar mai da hankali gadan-gadan a bisa neman kai karshen yakin. Bayan kammala taron dai ministan tsaro na Najeriyar Janar Mansur Dan'Ali mai ritaya ya ce za a ci gaba da yakar kungiyar ta Boko Haram har sai an kawo karshe su. Masu lura da al'ammura na ganin cewar wannan sabon yunkuri zai taimaka wajan rage ywan hare-haren da kungiyar ta Boko Haram ke kai wa.

Sauti da bidiyo akan labarin