Najeriya: Sojoji sun kashe 'yan #EndSARS | Labarai | DW | 16.11.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Sojoji sun kashe 'yan #EndSARS

Jami'an rundunar sojojin Najeriya sun yi amfani da harsashi mai rai, yayin tarwatsa masu zanga-zangar #EndSARS a jihar Lagos cikin shekarar da ta gabata ta 2020.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, batun kisan maasu zanga-zangar ta #EndSARS na kunshe cikin rahoton bincike da aka mikawa gwamnatin jihar Lagos.

Duk da cewa ba a fitar da rahoton ga jama'a ba, amma kamfanin dillancin labaran na Reuters ya ce masu binciken sun siffanta abin da sojojin suka yi a shekarar da ta gabata a matsayin kisan gilla da sunan tarwatsa masu zanga-zangar ta #EndSARS da masu fafutuka suka shirya a kan zargin cin zarafi da jami'an 'yan sandan rundunar SARS ke yi a kasar.

Kawo yanzu dai hukumar soja da ta 'yan sandan kasar ba su ce uffan ba kan wannan sabon rahoton, sai dai a baya sun sha nanata cewa ba su yi amfani da harsashi mai rai ba. To amma masu rahoton sun ce sun ga alamun 'yan sanda sun yi kokarin boye wasu hujjojin irin tabargazar da jami'an tsaro suka yi a Lekki Toll Gate da ke Lagos din, inda aka yi wannan artabu.