Najeriya: Sojoji sun kara da ′yan Boko Haram | Labarai | DW | 14.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Sojoji sun kara da 'yan Boko Haram

An shiga halin rudani yayin da wasu mayakan Boko Haram suka yi kokarin kwace iko da wani sansanin sojojin Najeriya da ke Mainok mai nisan kilomita 60 daga Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno.

Ba zato ba tsammani ne dai mayakan na Boko Haram suka bulla ta wani daji da ke hadewa da dajin Sambisa cikin motoci da babura suka nufi sansanin Sojoji da ke garin Mainok. An dai kwashe sa'o'i hudu ana ba ta kashi tsakanin mayakan da sojojin Najeriya inda wata majiya ta ce sun samu kutsawa cikin sansanin sojoji. Abin da ya sa mazauna garin na Mainok suka fantsama cikin daji don neman tsira. To sai dai Sojojin sun samu nasarar dakile harin tare da fatatakar mayakan na Boko Haram bayan sun samu taimako daga runduna ta bakwai ta sojoji daga Maiduguri. Wasu matafiya da lamarin ya rutsa da su a kan hanyarsu ta zuwa Damaturu daga Maiduguri sun bayyana cewar sun ga mayakan na Boko Haram cikin kayan damara irin na soji sai dai babu takalma a kafafunsu.


 

 

 

Sauti da bidiyo akan labarin