Najeriya: Shekaru biyar da sace ′yan mata Chibok | Labarai | DW | 14.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Shekaru biyar da sace 'yan mata Chibok

A Najeriya a kwana a tashi yau shekaru biyar kenan da Kungiyar Boko Haram ta sace 'yan matan sakandaren garin Chibok su 276 'yan shakaru 12 zuwa 17 a makarantar kwana ta garin

A Najeriya a kwana a tashi yau shekaru biyar kenan da Kungiyar Boko Haram ta sace 'yan matan sakandaren garin Chibok su 276 'yan shakaru 12 zuwa 17 a makarantar kwana ta garin a cikin daren 13 washe garin 14 ga watan na Aprilu inda suka zuba su a cikin motoci suka kutsi daji da su. 

Tun a wannan rana dai 57 daga cikin wadannan 'yan mata sun yi nasarar kubucewa bayan da suka yi kasadar dirowa daga motocin da ke dauke da su ana cikin tafiya. Labarin sace wadannan 'yan mata da kuma musamman faifayin bidiyonsu da kungiyar ta Boko Haram ta wallafa sun dimauta duniya. 

A karkashin mulkin Shugaba Buhari wanda ya dare karagar mulkin Najeriyar shekara daya bayan sace 'yan matan, gwamnatinsa ta yi nasarar karbo 107 daga cikinsu a karkashin wata yarjejeniya ta musayar fursunoni da kungiyar ta Boko Haram, wasunsu kuma sojoji ne suka tsinto su bayan da suka yi nasarar tserewa daga wuraren da kungiyar ke tsare da su. Ya zuwa yanzu dai akwai sauran 112 daga cikin wadannan 'yan mata da ba a da labarinsu, da kuma iyayensu ke ci gaba da neman sanin makomarsu.