1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Shekaru 57 na 'yanci da kalubale

Ahmed Salisu
September 29, 2017

Yayin da Najeriya ke cika shekaru 57 da zama 'yantacciyar kasa, rigingimu da dama na kokarin dagulawa kasar lissafi ciki kuwa har da kokarin ballewar yankin Igbo da nufin girka kasar Biafra.

https://p.dw.com/p/2kzNm
Karikatur von Abdulkareem Baba Aminu- Nigerias Unabhängigskeit

Wannan rikici na ballewar yankin Igbo daga kasar abu ne da ya jima ana yinsa sai dai lamari ya kara daukar zafi a dan tsakanin nan inda kungiyar nan ta IPOB ta zafafa fafutuka ta ganin yankin ya balle daga Najeriya, batun da hukumomin kasar ke ta fadi-tashin ganin an kawar da shi yayin da gwamnonin yankin kabilar Igbo a nasu bangaren ke kokari wajen ganin al'ummar yankin ta samu makoma mai kyau ta hanyar sauya musu tunani da kuma tallafa musu kan sanaoi da za su fishshe su maimakon fafutukar da suke yi ta kafa kasarsu ta Biafra.

Nigeria pro-Donald-Trump-Kundgebung der Indigenous People of Biafra in Port Harcourt
'Yan kungiyar IPOB na ragin ballewa daga Najeriya don kafa kasar BiafraHoto: Getty Images/AFP

Tuni dai gwamnan Jahar Ebonyi Chief Dave Umahi da ke zaman shugaban kungiyar gwamnonin yankin na Igbo su 5 ya fidda wannan sanarwa cewar sun kammala shiri na fara bada horon sauya hali da tunani da kuma akida ga dimbin matasa a yankin da ke tada hankula kan rajin kafa kasar Biafra kuma daga bisanin wannan horo shirin ya nuna cewar gamnonin za su ba matasan tallafi don fara sanaoi da zasu fishshe su a rayuwa. Wannan matakin na zuwa ne bayan da hukumomi a Najeriya suka haramta aikin kungiyar, batun da su ma shugabannin yankin suka ce girka kasar ta Biafra ba zai yiwu ba don a cewarsu Najeriya kasa daya ce, al'umma daya.

Nigeria Boko Haram Abubakar Shekau Archiv
Tada kayar Boko Haram ta sanya wasu yankuna Najeriya komawa karkashinsu amma daga baya gwamnati ta kwato suHoto: picture alliance/AP Photo

Wani kalubale har wa yau da ke barazana ga kasar shi ne na tsaro wanda bangaren arewacin kasar ya fuskanta a shekarun da suka gabata. Wannan matsala musamman ta Boko Haram ta jawo asarar rasuwar dubban mutane da asarar dukiya mai dumbiyawa kana wani bangare na kasar ya koma karkashin ikon 'yan Boko Haram ko da dai daga baya dakarun kasar sun yi amfani da karfin tuwo wajen maida yankunan karkashin ikon gwamnati. Wannan batu dai ya sanya zaman zullumi a kasar sannan mahukuntan Abuja kadu da irin yanayin da aka shiga.