1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Samun dan takarar indefenda a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
May 24, 2023

Majalisar dokokin Najeriya ta amince da kudurin dokar da zai samar da dan takara mai zaman kansa a tsarin zabe, wanda ba sai jam'iyya ta tsayar da shi ba kamar yadda yake yanzu a kasar.

https://p.dw.com/p/4RlGu
Najeriya | Siyasa | Zabe l Takara
Majalisun dokokin Najeriya, sun amince da dokar tsayawa takara karkashin indifendaHoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Haka ce ta kama hanyar cimma ruwa ta 'yan siyasa musamman matasa da suka dade suna rajin ganin an ba su dama ta tsayawa takara a karkashin indifenda, yunkurin da tun bayan sake kafa dimukuradiyya a 1999 ake yin sa a Najeriyar. Hakan dai ba ya rasa nasaba da yadda masu kudi a hannu suka kwace jamiyyun, duk cancantar dan siyasa bai isa ya tsaya takara ba sai da amincewarsu. An ci gaba da haka duk da rage shekarun tsayawa takara da aka yi, domin dole sai jam'iyya ta tsayar da mai son tsayawa takara kafin yin haka. Majalisun datawa da ta wakilai, bakinsu ya zo daya a kan dokar. A lokutan baya dai, rashin samun dama na dan takara mai zaman kansa ya katse hanzarin 'yan siyasa da dama a Najeriyar.

Najeriya | Zabe | Asiwaju Bola Ahmed Tinubu | Rabiu Musa Kwankwaso | Atiku Abubakar
A yanzu dai, tilas kowanne dan takara ya tsaya karkashin jam'iyyar siyasa

Samar da wannan doka dai gyaran fuska ne aka yi ga sashi na 58 na kundin tsarin mulkin Najeriyar da majalisun dokoki na jihohi 24 suka amince da shi, abin d ya bai wa majalisar dokokin ikon aiwatar da wannan gyara. Tuni dai matasa 'yan siyasa da sune suka gabatar da bukatar a majalisar, suka bayyana murna a kan haka. To sai dai wani hanzari ba gudu ba, kwararru na bayyana bukatar fitar da igantaccen tsari domin kaucewa yamutsa al'ammura na takara da ba zai yi wa tsarin zaben Najeriyar kyau ba. Abin jira shi ne shugaban kasar da ya rage masa 'yan kwanaki ya rattaba hannu a kan wannan kudiri, domin zama doka a Najeriyar.