Najeriya: Ruwan sama ya halaka Mutum 49 | Labarai | DW | 16.07.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Ruwan sama ya halaka Mutum 49

Ambaliyar ruwa ta haddasa asarar rayukan mutane akalla 49 a wasu kauyuka da ke karamar hukumar Jibiya a jahar Katsina a yankin arewacin Najeriya.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya daga daren ranar Lahadi ya zuwa Litinin ne ya janyo tunbatsar madatsar ruwan Tiga dam, wanda ya haifar da munmunar ambaliya a kauyukan da ke karamar hukumar ta Jibiya.

Amin Waziri shi ne sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa a jahar, ya tabbatar da faruwa lamarin da kuma kokarin da gwamnati ke yi na isar da taimako ga mabukata. Wasu kafafen yada labarai a jahar sun ce gidaje fiye da casa'in ne suka salwanta a sanadiyar iftala'in, baya ga asarar dabbobi sama da dari biyu da sittin. A na ci gaba da neman wasu mutanen da iyalansu ba su ji duriyarsu ba tun faruwar lamarin.